Jami'ar Tazkiyah Ta Bude Neman Guraben Karatu na Zangon shekaran 2026/2027

Jami'ar Tazkiyah Ta Bude Neman Guraben Karatu na Zangon shekaran 2026/2027

Jami'ar Tazkiyah da ke Zaria ta sanar da fara karɓar buƙatun neman guraben karatu na digiri na farko (Undergraduate) na shekarar 2026/2027.

A cikin sanarwar da jami'ar ta fitar, ta bayyana cewa masu neman gurbin karatu da suka cika ƙa'idojin shiga jami'ar za su iya neman shiga fannonin karatu daban-daban da jami'ar ke bayarwa.

Daga cikin kwasa-kwasan da ake da su akwai 
Nursing Sciences, 
Medical Laboratory Science, 
Public Health, 
Human Nutrition and Dietetics, Computer Science, 
Cyber Security, 
Software Engineering, 
Information Technology, Accounting, 
Economics, 
Business Administration da Taxation.

Jami'ar, wadda ke amfani da taken "Haɗa Ilimi da Kyawawan Ɗabi'u" (Blending Knowledge with Noble Characters), ta buƙaci masu sha'awar neman gurbin karatu da su yi rajista ta hanyar shafinta na yanar gizo.

Haka kuma, jami'ar ta ce masu neman ƙarin bayani za su iya ziyartar shafin rajistar ta ko kuma su tuntubi jami'ar ta lambobin wayar da aka bayyana a cikin sanarwar.

Jami'ar Tazkiyah tana garin Zariya na Jihar Kaduna, kuma tana da burin samar da ingantaccen ilimi tare da gina ɗalibai masu kyawawan ɗabi'u da ƙwarewar aiki.

0 $type={blogger}: