Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da aikin gyaran manyan hanyoyi wadanda zasu lashe Naira biliyan 137 a Jihar Borno, yana mai bayyana cewa aikin zai inganta harkokin kasuwanci da noma da kuma tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu a wajen bikin ƙaddamar da aikin a ranar Asabar, ya ce gyaran hanyar Bama zuwa Banki da kuma hanyar Dikwa zuwa Gamboru-Ngala zai dawo da muhimman hanyoyin kasuwanci tsakanin Najeriya da ƙasashen Kamaru da Chadi, waɗanda suka samu cikas sakamakon hare-haren 'yan ta'adda.
Tinubu ya ce lalacewar hanyoyi na kawo barazana ga tsaro, yana mai jaddada cewa ingantattun hanyoyi za su sauƙaƙa zirga-zirgar jama'a da kayayyaki tare da bai wa jami'an tsaro damar gudanar da sintiri cikin sauƙi.
Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce kamfaninsa ne ke aiwatar da ayyukan ƙarƙashin shirin gwamnatin tarayya na Roads Infrastructure Tax Credit Scheme. Ya bayyana cewa kamfanin na gudanar da manyan ayyukan hanyoyi guda 12 da suka zarce kilomita 1,000 a faɗin ƙasar, waɗanda darajarsu ta kai kusan Naira tiriliyan 3.
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa an fara ba da kwangilar ayyukan ne tun shekarar 2021 kan kuɗin kusan Naira biliyan 55, amma matsalolin tsaro da hauhawar farashin kayayyaki suka janyo sake duba kuɗin. Ya ce yanzu hanyar Bama zuwa Banki za ta ci Naira biliyan 70, yayin da hanyar Dikwa zuwa Gamboru-Ngala za ta ci Naira biliyan 67.
Umahi ya ce za a gina hanyoyin ne da fasahar siminti mai ɗorewa domin rage yawan gyare-gyare da tsawaita rayuwar hanyoyin.
Ya ƙara da cewa aikin ya haɗa da gina gadoji da sanya kayan tsaron hanya da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce ayyukan za su taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin jihar da ƙarfafa kasuwanci da ƙasashen Chadi da Kamaru da Nijar, tare da tallafa wa ƙoƙarin dawo da zaman lafiya bayan shekaru na matsalar rashin tsaro.

0 $type={blogger}:
Post a Comment