Akalla mutane 30 ne, ciki har da yara takwas, suka rasa rayukansu bayan wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne suka kai hari kauyen Naridon da ke Kamaru Ward na karamar hukumar Kauru a Jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin kauyen ne da misalin karfe 11:00 na daren Lahadi, inda suka rika harbe-harbe kan mai uwa da wabi tare da kona gidaje.
Haka kuma, mutane da dama sun jikkata sakamakon harin.
Magatakardar Mai Unguwar Naridon, Dogon Rana, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 30, yayin da wasu mutum hudu ke karbar magani saboda munanan raunuka.
Ya bayyana cewa harin ya kasance daya daga cikin mafi muni da al'ummar kauyen suka taba fuskanta, inda ya ce iyalai da dama sun rasa 'yan uwansu tare da lalacewar dukiyoyi na miliyoyin naira.
Rana ya ce wani mazaunin kauyen ya rasa 'ya'yansa biyar a dare guda, yayin da yaro daya tilo da ya tsira ke fama da munanan raunuka a asibiti. Ya kuma bayyana cewa gidansa da shaguna da dama sun kone sakamakon harin.
Ya ce rashin kyakkyawar hanyar mota zuwa kauyen ya jinkirta isowar jami'an ceto, lamarin da ya kara yawan asarar rayuka.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin tsaro da su kara tura jami'an tsaro tare da gina hanyar mota zuwa kauyen domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya yi zargin cewa mutum 22 daga cikin iyalan Rana sun mutu a harin. Ya kuma ce harin ya dauki kusan sa'o'i uku ana kaiwa ba tare da jami'an tsaro sun kawo dauki ba, duk da kasancewar sansanonin sojoji a yankunan da ke kusa.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba, domin ba a samu nasarar jin ta bakin kakakin rundunar ba.
Source: Punch News.

0 $type={blogger}:
Post a Comment