Akalla mutane 107 ne suka rasa rayukansu, yayin da 344 suka jikkata sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa da ta addabi sassan ƙasar Pakistan tun bayan fara daminar bana, kamar yadda Hukumar Kula da Bala'o'i ta Kasar (NDMA) ta bayyana.
Rahoton ya ce mafi yawan wadanda suka mutu sun rasu ne sakamakon rushewar gidaje da rufinsu. Lardin Khyber Pakhtunkhwa ne ya fi yawan mace-mace da mutum 55, sai Punjab da mutum 36.
A lardin Punjab, ambaliyar ruwa ta mamaye yankuna da dama, musamman a biranen Lahore da Gujranwala, lamarin da ya sa gwamnatin ƙasar ta kafa sansanonin agaji 17 domin karbar mutanen da suka rasa matsugunansu.
Babbar Ministar Punjab, Maryam Nawaz Sharif, ta ce an tura jami'an agajin gaggawa domin taimakawa al'ummomin da ambaliyar ta shafa tare da ci gaba da kokarin fitar da ruwan ambaliyar.
Hukumar Hasashen Yanayi ta Pakistan ta yi gargadin cewa ana sa ran wani sabon zagayen ruwan sama mai karfi zai fara daga ranar Laraba, wanda ka iya haddasa karin ambaliya a Islamabad da Punjab ta sama da Yankin Kashmir na Pakistan da Khyber Pakhtunkhwa da Gilgit-Baltistan.
Mahukunta sun bukaci mazauna yankunan da ke fama da barazanar ambaliya su kasance cikin shiri tare da bin umarnin hukumomi, yayin da ake sa ran daminar za ta ci gaba har zuwa watan Satumba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment