Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da kama wani soja, Mohammed Yusuf, wanda aka ayyana ana nema ruwa a jallo bisa zarginsa da safarar kayan aikin soja ga 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka.
A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Jami'in Yada Labarai na Operation Hadin Kai, Kyaftin Muhammed Goni, ya fitar, an ce dakarun 7 Provost Group ne suka kama sojan a tashar motoci ta Jidari da ke Maiduguri, Jihar Borno, a ranar 25 ga Yuli, 2026, yayin da ake zargin yana kokarin tsallakawa zuwa Jamhuriyar Kamaru.
Sanarwar ta ce sojan, wanda ke aiki a Nigerian Army Ordnance Kits Factory da ke Legas, an ayyana ana nemansa tun ranar 23 ga watan Yuli, 2026.
Binciken farko ya nuna cewa ya tsere daga sansaninsa tun ranar 7 ga watan Yuli, sannan ya buya a unguwar Gomari Costain da ke karamar hukumar Jere tare da taimakon wani abokinsa.
Rundunar ta ce an kama shi ne bayan samun sahihan bayanan sirri, a wani bangare na kokarin dakile hanyoyin da ke bai wa 'yan ta'adda tallafi da kayan aiki.
A halin yanzu, ana tsare da wanda ake zargin a hannun 7 Provost Group, inda ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken rawar da ya taka da kuma ko akwai wasu da suka hada baki da shi.
Kyaftin Goni ya jaddada cewa Rundunar Sojojin Najeriya za ta ci gaba da tabbatar da gaskiya da ladabtarwa da kuma hukunta duk wanda aka samu yana taimakawa ta'addanci ko sauran ayyukan ta'addanci, ba tare da la'akari da matsayinsa ba.
Haka kuma ya bukaci al'umma su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment