Shugaban Kasar Bangladesh Ya Yi Murabus Saboda Rashin Lafiya

Shugaban Kasar Bangladesh Ya Yi Murabus Saboda Rashin Lafiya

Shugaban kasar Bangladesh, Mohammed Shahabuddin, ya yi murabus daga mukaminsa, yana mai bayyana cewa tabarbarewar lafiyarsa ce ta tilasta masa daukar wannan mataki.

Shahabuddin mai shekaru 76 ya tabbatar da murabus dinsa a ranar Juma'a, inda ya kawo karshen rade-radin cewa zai sauka daga mulki kafin karewar wa'adinsa a shekarar 2028.

A cikin wasikar murabus da ya aikawa Kakakin Majalisar Dokokin kasar, ya bayyana cewa tabarbarewar lafiyar jikinsa da ta kwakwalwarsa ta sa ba zai iya ci gaba da gudanar da nauyin ofishin shugaban kasa yadda ya kamata ba.

An zabi Shahabuddin a matsayin shugaban kasa a shekarar 2023 tare da goyon bayan jam'iyyar Awami League ta tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina. 
Bayan hambarar da gwamnatin Hasina sakamakon zanga-zangar dalibai a shekarar 2024, an fara kiraye-kirayen cewa shi ma ya sauka daga mukaminsa.

A baya, shugaban ya musanta zargin cewa ya tattauna da Sheikh Hasina ta wayar tarho yayin da yake jinya a birnin London.

Kafin tabbatar da murabus din, Ministan Harkokin Cikin Gida na Bangladesh, Salahuddin Ahmed, ya ce gwamnati ba ta samu wata sanarwa a hukumance daga shugaban kasar ba. 
Kundin tsarin mulkin Bangladesh ya tanadi cewa shugaban kasa dole ne ya mika takardar murabus ga Kakakin Majalisar Dokoki kafin murabus dinsa ya fara aiki.

Murabus din Shahabuddin na zuwa ne a wani lokaci da Bangladesh ke ci gaba da fuskantar sauye-sauyen siyasa bayan ficewar tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina daga mulki.

0 $type={blogger}: