Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi a Kudancin Kaduna, yana mai cewa lamarin ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Litinin, Atiku ya bayyana harin da aka kai a Ƙaramar Hukumar Kauru da cewa abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba.
Ya ce duk rayuwar da aka rasa tana nuna gazawar gwamnati wajen cika nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kare jama'a.
Atiku ya soki gwamnatin Tinubu, yana zargin wasu manyan jami'an gwamnati da mayar da hankali kan abin da ya kira yabon ƙasashen waje maimakon magance matsalar tsaron da ke ci gaba da addabar Najeriya.
Ya kwatanta yadda gwamnatin Amurka ta kashe kusan dala 750,000 domin ceto wani ɗan ƙasarta da ya makale, yana mai cewa hakan ya nuna yadda gwamnati ke daraja rayuwar kowane ɗan ƙasa.
Ya ce abin da 'yan Najeriya ke buƙata ba yabo daga ƙasashen waje ba ne, illa ingantaccen tsaro da zai ba su damar kwanciyar hankali da yin tafiye-tafiye da noma da gudanar da harkokinsu ba tare da tsoron hare-haren 'yan ta'adda da 'yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ba.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi kira da a sake fasalin tsarin tsaron ƙasa baki ɗaya, tare da ƙarfafa tattara bayanan sirri da gaggauta hukunta masu aikata laifuka da ɗaukar matakan kariya domin hana sake faruwar irin waɗannan hare-hare.
Haka kuma, Atiku ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu da al'ummar Kudancin Kaduna, yana addu'ar Allah Ya gafarta wa mamatan tare da bai wa waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.
Ya buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike, su kamo tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a harin, sannan su ƙara tsaurara matakan tsaro a yankunan da ke cikin haɗari yayin da ƙasar ke tunkarar wani sabon lokacin siyasa.
A cewarsa, tarihi zai tuna da gwamnati ne bisa yadda ta kare rayuka da dukiyoyin jama'arta, ba wai bisa ikirarin samun yabo daga ƙasashen waje ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment