'Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Mutuwar Wani Tsoho Mai Shekara 60 a Otel a Jigawa.

'Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Mutuwar Wani Tsoho Mai Shekara 60 a Otel a Jigawa.

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Jigawa ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wani mutum mai shekaru 60 da ya rasu a wani otel da ke Dutse bayan ya kamu da rashin lafiya yayin da yake tare da wata budurwa mai shekaru 20.

Kakakin rundunar, SP Shi'isu Adam, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:50 na ranar 21 ga Yulin 2026. A cewarsa, mutumin ya shiga otel tare da budurwar, sannan bayan ya nemi abinci kuma ya ci, sai ya fara fama da matsananciyar rashin lafiya.

Da samun rahoton abin da ya faru, jami'an 'yan sanda daga Sashen Yalwawa suka garzaya wurin tare da kai mutumin Asibitin Koyarwa na Dutse domin ceto rayuwarsa, amma likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

A yayin binciken farko, jami'an bincike sun kwato wasu kayan abinci da abubuwan sha da wani magani da ake zargin na ƙara ƙarfin jima'i ne, tare da wasu kayayyakin mutumin domin ci gaba da bincike.

Bayan kammala dukkan matakan da suka dace, an mika gawar mamacin ga iyalansa domin yi masa jana'iza.

Rundunar ta ce budurwar mai shekaru 20 da ke tare da mamacin tana ba jami'an tsaro cikakken haɗin kai tare da bayar da bayanan da za su taimaka wajen gano musabbabin mutuwar.

Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Jigawa ya tabbatar wa al'umma cewa za a gudanar da binciken cikin adalci da ƙwarewa da gaskiya, tare da yin kira ga jama'a da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba yayin da bincike ke ci gaba.

Rundunar ta ce za ta sanar da jama'a duk wani sabon ci gaba da zarar binciken ya kammala.

0 $type={blogger}: