Mutane 26 ne Suka Mutu Yayin da Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Wasu Sassan ƙasar Indiya.

Mutane 26 ne Suka Mutu Yayin da Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Wasu Sassan ƙasar Indiya.

Akalla mutane 26 ne suka rasa rayukansu sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa mummunar ambaliyar ruwa a jihar Assam da ke arewa maso gabashin Indiya.

Mahukuntan jihar sun bayyana cewa mutane 21 sun mutu ne a ranar Talata bayan ambaliyar ta mamaye garuruwa da dama, lamarin da ya kai yawan wadanda suka mutu a cikin makon nan zuwa 26.

Kogin Brahmaputra, daya daga cikin manyan koguna a duniya, ya haura matakin hadari a wasu yankuna, lamarin da ya kara tsananta ambaliyar.

Ruwan saman ya kuma janyo zaftarewar kasa a kan babbar hanyar Jammu zuwa Srinagar, wanda ya tilasta rufe hanyar ga ababen hawa. Haka kuma an dakatar da aikin hajjin Kedarnath a wasu wurare bayan manyan duwatsu sun fado kan hanyar mahajjata, inda aka kwashe su zuwa wurare masu aminci.

Hukumar hasashen yanayi ta Indiya ta yi gargadin cewa ana sa ran karin ruwan sama mai karfi da tsawa da iska mai karfi a jihohin Assam da Gujarat da Himachal Pradesh da Jammu da Kashmir.

A halin yanzu jami'an agaji da hukumomin gwamnati na ci gaba da gudanar da ayyukan ceto tare da gargadin jama'a kan yiwuwar karin ambaliya da zaftarewar kasa.

0 $type={blogger}: