Jami'ar Tarayya Ta Wukari Ta Haramta Bukukuwan "Sign-out" A Harabarta.

Jami'ar Tarayya Ta Wukari Ta Haramta Bukukuwan "Sign-out" A Harabarta.

Hukumar gudanarwar Jami'ar Tarayya ta Wukari (FUW) da ke jihar Taraba ta haramta duk wani nau'in bikin kammala karatu da ake kira "sign-out" da kuma jerin gwano a harabar jami'ar da kewaye.

An amince da wannan mataki ne a taron Majalisar Dattawan Jami'ar (Senate) karo na 76, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jami'ar, Farfesa Benjamin Ate Kefas, domin ƙarfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya da kuma kiyaye doka da oda a harabar jami'ar.

Sabuwar dokar ta haramta sanya hannu a riguna (T-shirts) da jerin gwano da rawa da likin kuɗi da shirya bukukuwa, da zirga-zirgar ayarin motoci da ke da alaƙa da bikin kammala karatu a cikin harabar jami'ar da kewayenta.

Haka kuma, jami'ar ta hana taruka a ƙofar jami'a da kuma kan titin Katsina-Ala zuwa Jalingo, tana mai cewa irin waɗannan tarukan na haddasa cunkoson ababen hawa da hargitsi da kuma barazana ga rayuka da dukiyoyi.

Mahukuntan jami'ar sun umarci jami'an tsaro su tabbatar an bi wannan dokar, tare da ɗaukar matakin ladabtarwa kan duk wanda ya karya ta bisa ƙa'idodin jami'ar.

Jami'ar ta kuma yi kira ga ɗalibai da iyaye da masu kula da ɗalibai da tsofaffin ɗalibai da sauran jama'a da su ba da haɗin kai wajen bin wannan sabon tsari domin samar da ingantaccen yanayin karatu cikin aminci da kwanciyar hankali.

0 $type={blogger}: