Rundunar 'Yan Sandan Jihar Nasarawa ta sanar da cewa ta dakile wani yunkurin sace mutane tare da ceto mutane hudu ba tare da sun ji rauni ba, a wani samame da jami'anta suka gudanar a yankin Andaha da ke Karamar Hukumar Akwanga.
Kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:40 na daren ranar 21 ga watan Yuli, 2026, bayan sun samu kiran gaggawa cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suna yunkurin sace mutane a kusa da gidan mai na Megona da ke kan hanyar Akwanga zuwa Jos.
Ya ce da samun rahoton, DPO na sashen Andaha ya jagoranci tawagar jami'an tsaro zuwa wurin. Da masu garkuwar suka hangi 'yan sanda, sun bude musu wuta, lamarin da ya haifar da musayar harbe-harbe.
Sai dai jami'an 'yan sanda sun yi nasarar fatattakar maharan da karfin wuta, wanda ya tilasta musu tserewa cikin daji da raunuka daban-daban, tare da barin mutanen hudu da suka yi garkuwa da su. Dukkan wadanda aka ceto ba su samu wani rauni ba.
Har ila yau, jami'an tsaron sun kwato wasu kayayyakin abinci da ake kyautata zaton an sace su ne daga wani shagon sayar da kayan masarufi.
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Nasarawa, CP Shetima Jauro Mohammed, ya yabawa jami'an da suka gudanar da aikin saboda jarumtaka da kuma saurin daukar mataki.
Ya kuma bayar da umarnin a ci gaba da farautar wadanda suka tsere tare da amfani da dukkan hanyoyin tattara bayanan sirri domin cafke su da gurfanar da su a gaban kuliya.
Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da samamen hadin gwiwa da sojoji da masu sa-kai da mafarauta domin kamo wadanda ake zargi, tare da rokon al'umma da su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai domin yaki da miyagun laifuka a fadin jihar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment