Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace shugaban makarantar Nomadic Basic School da ke Igbojaye, karamar hukumar Itesiwaju a Jihar Oyo, Malam Matthew Kolawale Owoade mai shekaru 60, tare da neman kudin fansa har Naira miliyan 30 domin sakinsa.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar yayin da shugaban makarantar ke dawowa daga gonarsa, inda maharan suka tare shi suka tafi da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
A cewar ɗansa, Abiola Owoade, bayan sace mahaifinsa, masu garkuwar sun kira iyalan ta amfani da wayarsa tare da neman a biya Naira miliyan 30 kafin su sake shi.
Da safiyar Lahadi, masu bincike sun gano babur ɗin shugaban makarantar da aka jefar a cikin wani daji, amma har yanzu ba a gano inda yake ba.
Lamarin ya jefa iyalansa da abokan aikinsa da al'ummar yankin cikin damuwa, inda suka roƙi jami'an tsaro su ƙara kaimi wajen ceto shi cikin koshin lafiya tare da kamo waɗanda suka aikata wannan ta'asa.
Mai magana da yawun Rundunar 'Yan Sandan Jihar Oyo, DSP Olayinka Ayanlade, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami'an tsaro sun fara bincike tare da gudanar da aikin ceto domin kubutar da shugaban makarantar ba tare da wata illa ba da kuma cafke masu garkuwar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment