Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin karin kudin rajistar jarabawar WAEC da NECO na shekarar 2027, bayan korafe-korafe da martanin da jama'a suka nuna kan shirin.
Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ta bayyana cewa ta janye wasikar da ta fitar a ranar 18 ga watan Yuni, 2026, wadda ta sanar da shirin karin kudin rajistar, domin ba da damar yin cikakken tuntuba da masu ruwa da tsaki.
Ma'aikatar ta ce an fara tunanin karin kudin ne saboda hauhawar farashin gudanar da jarabawar kasa, ciki har da sufuri da tsaro da buga takardun jarabawa da amfani da fasaha da kuma tabbatar da ingancin tsarin gudanar da jarabawa.
Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya bayar da umarnin dakatar da shirin domin bai wa gwamnati damar tattaunawa da hukumomin gudanar da jarabawa da ma'aikatun ilimi na jihohi da masu makarantu da kungiyoyin iyaye da kungiyoyin kwadago da sauran masu ruwa da tsaki.
Ma'aikatar ta jaddada cewa ba za a aiwatar da karin kudin rajistar WAEC da NECO ba har sai an kammala shawarwari tare da yanke hukunci na karshe.
Gwamnatin Tarayya ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da ba da fifiko ga inganta ilim da tabbatar da damar samun ingantaccen ilimi ga kowa, da kuma gudanar da manufofi cikin gaskiya da adalci.

0 $type={blogger}:
Post a Comment