Tinubu Ya Umarci NIMC Ta Yi Wa Dukkan 'Yan Najeriya Rijistar NIN Kafin Karshen 2026

Tinubu Ya Umarci NIMC Ta Yi Wa Dukkan 'Yan Najeriya Rijistar NIN Kafin Karshen 2026

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Kula da Bayanan Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC) da ta tabbatar da cewa an yi wa dukkan 'yan Najeriya rijistar Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) kafin ƙarshen shekarar 2026.

Darakta Janar kuma Babbar Jami'ar Hukumar NIMC, Abisoye Coker-Odusote, ta bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Channels Television, inda ta ce umarnin na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na gina cikakken tsarin tantance 'yan ƙasa domin inganta shugabanci da tsare-tsare da kuma isar da ayyukan gwamnati.

Ta bayyana cewa NIMC na haɗin gwiwa da masu rajista masu zaman kansu ƙarƙashin shirin Identification for Development (ID4D) na Bankin Duniya domin hanzarta aikin rajistar NIN a faɗin ƙasar.

Coker-Odusote ta ce lambar NIN ita ce shaidar mutum ta musamman, wadda ke tabbatar da cewa mutum guda ba zai samu rajista fiye da ɗaya ba, ta hanyar amfani da bayanan halitta kamar yatsu da fuska.

Ta ƙara da cewa aikin zai taimaka wajen tantance ainihin yawan al'ummar Najeriya, domin a halin yanzu ana hasashen yawan jama'ar ƙasar na tsakanin miliyan 200 zuwa miliyan 250.

A cewarta, sabon tsarin zai ƙara inganta tsaro tare da hana yin rajista sau da yawa, yayin da hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu za su riƙa tabbatar da sahihancin bayanan jama'a kai tsaye ta hanyar haɗa tsarin su da na NIMC.

Umarnin ya biyo bayan rattaba hannun da Shugaba Tinubu ya yi kan Dokar NIMC ta 2026, wadda ta ƙarfafa manufar "Mutum Ɗaya, Shaida Ɗaya", tare da mayar da NIN a matsayin babbar shaidar da za a riƙa amfani da ita wajen samun muhimman ayyukan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, ciki har da harkokin banki da fasfo da haraji da fansho da mallakar ƙasa da samun bashi.

0 $type={blogger}: