Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Gombe ta jinkirta hukunci kan ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar, wadda ke kalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na PDP.
A yayin zaman shari'ar, lauyan jam'iyyar PDP ya roƙi kotu da ta yi watsi da ƙarar, yana mai cewa ba ta cika ka'idojin doka ba kamar yadda Sashe na 115 na Dokar Shaidu ya tanada.
Shi ma lauyan Pantami ya buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar, yana mai cewa Pantami ya yi murabus daga jam'iyyar APC a ranar 19 ga Mayu, 2026, kafin ya shiga zaɓen fidda gwani na PDP.
A nasa bangaren, lauyan mai ƙara ya ce sun gabatar da takardun martani, hujjoji da sauran bayanan da ke nuna cewa ƙarar ta cancanci a saurare ta. Ya kuma roƙi kotun ta yi watsi da duk ƙorafe-ƙorafen farko da waɗanda ake ƙara suka gabatar.
Bayan sauraron dukkan ɓangarorin, Mai Shari'a Amina Aliyu Mohammed ta jinkirta hukunci, inda ta ce za a sanar da ɓangarorin ranar da za a yanke hukuncin.

0 $type={blogger}:
Post a Comment