'Yan bindiga sun kashe manoma tara, tare da yin garkuwa da wasu da dama a jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun kashe manoma tara, tare da yin garkuwa da wasu da dama a jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun kashe akalla manoma 9 tare da yin garkuwa da wasu da dama a wani hari da suka kai kan gonaki da ke ƙauyen Kakangi, a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne a ranar Asabar inda suka bude wa manoman da ke aiki a gonakinsu wuta. 
An gano gawarwaki tara, yayin da hukumomin yankin suka tabbatar da tantance shida daga cikinsu. Wani jagoran al'umma a Birnin Gwari, Kabiru Ishaq, ya ce adadin waɗanda aka kashe ya kai mutum goma.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya biyo bayan kashe wani ɗan bindiga da wasu manoma suka yi ne lokacin da ya yi yunƙurin kai musu hari. Bayan mutuwar ɗan bindigar, abokan aikinsa sun dawo da ƙarin mayaƙa tare da kai harin ramuwar gayya.

Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin hukumomin yankin da 'yan bindiga tun watan Nuwamban 2024, yankin Birnin Gwari na ci gaba da fuskantar hare-hare. A watan da ya gabata ma, an kashe manoma shida tare da sace kusan mutum 20 a ƙauyen Danauta.

A baya-bayan nan, hare-haren 'yan bindiga sun ƙaru a al'ummomin manoma da ke arewaci da tsakiyar Najeriya, inda suke kashe mutane da yin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa tare da satar dabbobi da kuma wawashe dukiyoyi.

0 $type={blogger}: