Miliyoyin mutane ne suka taru a babban birnin ƙasar Iran, Tehran, domin halartar jana'izar tsohon Jagoran Addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamene'i, wanda aka kashe a hare-haren da Amurka da Isra'ila ta kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu, lamarin da ya tayar da yaƙin da ya ɗauki watanni tsakanin ɓangarorin biyu.
Masu makoki sun cika manyan titunan birnin sanye da baƙaƙen kaya, suna ɗauke da tutocin Iran da hotunan Khamene'i, yayin da ake gudanar da jerin bukukuwan bankwana kafin a kai gawarsa domin binne ta a Mashhad.

0 $type={blogger}:
Post a Comment