Wata yarinya mai suna Hauwa'u Sani ta rasa ranta bayan da ake zargin ta kashe kanta ta hanyar shan maganin fesa kwari (fiyà-fiyà), sakamakon hana ta auren saurayin da take so.
Bincike ya nuna cewa lamarin ya faru ne a garin Ƴankara, da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Wani mazaunin yankin, Fahad Danladi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce al'ummar yankin sun shiga jimami bayan wannan abin takaici.
Source: Rariya

0 $type={blogger}:
Post a Comment