Wata mata ta bayyana yadda ta haihu cikin barci ba tare da ta sani ba.

Wata mata ta bayyana yadda ta haihu cikin barci ba tare da ta sani ba.

Wata mata 'yar ƙasar Canada mai shekaru 27, Carolina Moreno, ta bayyana yadda ta haifi ɗanta na uku cikin barci ba tare da ita ko ma'aikatan jinya sun sani ba.

Moreno ta ce an kwantar da ita a asibiti domin a tayar mata da naƙuda bayan an gano tana ɗauke da ƙwayar cutar Group B Streptococcus, lamarin da ya sa likitoci suka ba ta maganin rigakafin haihuwa.

Bayan naƙuda ta tsananta, an yi mata allurar rage raɗaɗi, wanda ya sa ta samu sauƙin ciwo har ta yi barci.

Yayin da ma'aikatan jinya ke ci gaba da sa ido kan bugun zuciyar jaririn, sai suka kasa gano bugun, abin da ya tayar da hankalinsu. 

Da Moreno ta farka, ta yi tunanin wani mummunan abu ya faru da jaririn.

Sai dai lokacin da aka ɗaga bargon gadon, an gano cewa jaririn ya riga ya fito da kansa kuma yana kwance cikin shiru a ƙarƙashin bargon, ba tare da kowa ya lura da haihuwarsa ba.

Nan take ma'aikatan jinya suka ɗauki jaririn suka motsa shi har ya fara kuka. Moreno ta ce ita da mijinta da sauran 'yan uwanta sun yi matuƙar mamaki domin duk sun rasa lokacin da aka haifi jaririn.

Daga baya likitoci sun tabbatar da cewa jaririn ya fito da kansa ne yayin da mahaifiyarsa ke barci, kuma dalilin da ya sa aka kasa gano bugun zuciyarsa shi ne saboda ya riga ya fito daga cikin mahaifa.

Yanzu haka jaririn yana da watanni uku a duniya kuma yana cikin koshin lafiya. Moreno ta ce ɗanta yana da natsuwa sosai, abin da ya sa bai yi kuka nan take bayan an haife shi ba.

0 $type={blogger}: