Hare-haren Isra'ila Sun Kashe Mutane Takwas, Ciki Har da Yara Biyu a Gaza.

Hare-haren Isra'ila Sun Kashe Mutane Takwas, Ciki Har da Yara Biyu a Gaza.

Akalla mutane takwas ne, ciki har da yara biyu masu shekaru 10 da 6, suka mutu sakamakon hare-haren sama da sojojin Isra'ila suka kai a sassa daban-daban na Zirin Gaza a ranar Laraba, kamar yadda jami'an lafiya na Falasɗinu suka bayyana.

Rahotanni sun ce mutum daya ya mutu a kusa da wata makaranta a birnin Gaza, yayin da wani hari kan tantunan da ke ba da mafaka ga mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Al-Mawasi da ke Khan Younis ya kashe mutane hudu, ciki har da yaro dan shekara 10.

Haka kuma, wani yaro mai shekara shida ya mutu bayan harbin da ake zargin sojojin Isra'ila ne suka yi a unguwar Zeitoun da ke Gaza, yayin da wani mutum ya mutu a wani hari da aka kai kan wata mota a yammacin birnin.

Jami'an lafiya sun ce mutum 12 sun jikkata a hare-haren. 
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan mayakan Hamas a Zirin na Gaza, amma ta ce ba ta da cikakken bayani kan rahotannin asarar rayukan fararen hula.

Hare-haren sun faru ne duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta shiga tsakanin Isra'ila da Hamas a watan Oktoban 2025. 

Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ce sama da mutane 1,080 ne suka mutu, yayin da fiye da 3,490 suka jikkata tun bayan fara tsagaita bude wutar. 
Ta kuma bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu tun bayan fara yaƙin a watan Oktoban 2023 ya haura 73,000, yayin da sama da 173,000 suka jikkata.

A halin yanzu, hukumomin agaji na duniya suna ci gaba da gargadin cewa matsalar jin kai a Gaza na ƙara ta'azzara, sakamakon faɗaɗa yankunan da Isra'ila ke iko da su da kuma yawaitar cututtuka a sansanonin 'yan gudun hijira.

0 $type={blogger}: