Babban Hafsan Sojin Ƙasar Najeriya Ya Jagoranci bikin Yaye Sabbin Sojoji Sama da 3,000 a Jihar Ebonyi.

Babban Hafsan Sojin Ƙasar Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya Jagoranci bikin yaye sabbin sojoji sama da 3,000 da suka kammala horaswa a Cibiyar Horar da Sojoji ta Depot Nigerian

Babban Hafsan Sojin Ƙasar Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya Jagoranci bikin yaye sabbin sojoji sama da 3,000 da suka kammala horaswa a Cibiyar Horar da Sojoji ta Depot Nigerian Army da ke Amasiri-Edda, a Jihar Ebonyi.

Da yake jawabi yayin bikin yaye sojojin a ranar Laraba, Shaibu ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da ƙara yawan jami'an rundunar soji domin ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

Ya bayyana cewa an ba sabbin sojojin horo na musamman da zai ba su damar fuskantar yaƙe-yaƙen zamani da kuma sabbin barazanar tsaro. Haka kuma ya buƙace su da su kasance masu biyayya ga kundin tsarin mulkin ƙasa, masu ladabi, ƙwarewa da jajircewa wajen kare Najeriya.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, ya ce kafa cibiyar horaswar da ke Amasiri-Edda wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa tsarin horas da sojoji da kuma samar da ƙwararrun jami'an da za su taimaka a ayyukan tsaro a sassan ƙasar.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayyana cibiyar horaswar a matsayin wata babbar kadara ga ƙasa, yana mai cewa ta inganta tsaro, ta bunƙasa harkokin tattalin arziki, tare da samar da damammakin aiki ga al'ummar jihar da maƙwabtanta.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa kai da rundunar soji da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da ci gaban jihar.

Bikin yaye sojojin ya samu halartar manyan hafsoshin soja da jami'an gwamnati da sarakunan gargajiya da iyalan sabbin sojojin da sauran manyan baƙi. 
An kuma gudanar da fareti, nuna ƙwarewar sojoji da kuma bayar da lambobin yabo ga waɗanda suka fi fice a horon.

0 $type={blogger}: