Majalisar Dattawan Najeriya Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin maido da Tsofaffin 'Yan Boko Haram cikin Al'umma.

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin maido da Tsofaffin 'Yan Boko Haram cikin Al'umma.

Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da shirin gyaran hali da sake komawa da tsofaffin 'yan Boko Haram cikin al'umma, tana mai cewa duk wanda ake zargi da ta'addanci ya kamata a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa doka.

Kudurin ya biyo bayan wata muhimmiyar sanarwa da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Rundunar Sojoji, Sanata Abdulaziz Musa Yar'Adua, ya gabatar ne kan karuwar hare-hare da garkuwa da mutane da kashe jami'an soja masu aiki da kuma wadanda suka yi ritaya.

Sanatocin sun bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara ta'azzara a kasar, inda suka ce ta'addanci da tayar da kayar baya da fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran hare-haren Ta'addanci na ci gaba da hallaka mutane tare da lalata rayuwa da tattalin arziki.

Majalisar ta bukaci hukumomin tsaro su tabbatar da kama tare da gurfanar da duk masu hannu a hare-haren ta'addanci da sauran manyan laifuka.

Har ila yau, Majalisar ta yi zaman makoki na minti guda domin girmama marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar da sauran 'yan Najeriya da suka rasa rayukansu sakamakon ta'addanci da sauran matsalolin tsaro.

Majalisar ta kuma yanke shawarar aika tawagar sanatoci domin jajanta wa iyalan marigayin da Gwamnatin Jihar Katsina da Rundunar Sojin Najeriya.

Sanatocin sun yaba wa Rundunar Sojoji da sauran hukumomin tsaro da leken asiri saboda kokarinsu wajen kare kasa, tare da yin kira da a kara inganta tattara bayanan sirri da hadin gwiwa tsakanin hukumomi da tsarin sa ido da gargadin wuri da kuma amfani da fasahar zamani wajen yaki da rashin tsaro.

Sun kuma bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro da al'ummomi da sarakunan gargajiya da shugabannin addini domin inganta tattara bayanan sirri daga al'umma.

Sanata Joseph Ikpea ya ce shirin sake maido da tsofaffin 'yan Boko Haram cikin al'umma ya zama abin damuwa ga jama'a, yayin da Sanata Adams Oshiomhole ya jaddada cewa gwamnati ta fi mayar da hankali wajen tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa da hukunta masu laifi da kuma tallafa wa jami'an tsaro da iyalansu.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce ta'addanci matsala ce ta duniya da ke bukatar hadin gwiwar kasa da kasa, tare da yabawa jami'an tsaro kan kokarinsu da kuma kira ga 'yan Najeriya su ci gaba da mara musu baya.

0 $type={blogger}: