Gwamnatin Jihar Legas ta sanar da cewa za ta tantance tare da mayar da mabarata 396 da aka kama yayin wani samamen tsaftar muhalli zuwa jihohin da suka fito.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce jami'an Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli ta jihar Legas (KAI Corps) ne suka gudanar da samamen a matsayin wani bangare na kokarin gwamnati na tabbatar da tsafta, tsaro da bin doka a fadin jihar.
Wahab ya ce za a yi wa dukkan mutanen da aka kama rajista da tantancewa, sannan a ba su tallafin da ya dace kafin a mika su ga hukumomin da abin ya shafa domin mayar da su cikin aminci zuwa jihohin da suka fito.
Ya bayyana cewa matakin na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin jihar na inganta tsaftar muhalli da tabbatar da zaman lafiya da tsaro, tare da rage yawan bara a kan titunan Legas.
Gwamnatin Legas ta kuma sake tunatar da al'umma cewa yin bara a tituna haramun ne a karkashin dokokin jihar. Haka kuma, ta ce bai halatta a rika ba wa mabarata sadaka a manyan tituna ba, tana mai kira ga jama'a da su rika bayar da gudummawarsu ta hannun kungiyoyin agaji da cibiyoyin addini da aka amince da su.

0 $type={blogger}:
Post a Comment