Hukumar Ƙwallon Ƙafar Faransa (FFF) ta sanar da shirin gurfanar da ƴar majalisar dattawan Paraguay, Celeste Amarilla, bayan ta yi kalaman da suka kwatanta tauraron ɗan wasan Faransa, Kylian Mbappé, da biri, biyo bayan ficewar Paraguay daga gasar cin kofin duniya.
FFF ta bayyana kalaman a matsayin nuna wariyar launin fata da cin zarafi, tana mai jaddada cewa ba za ta lamunci irin waɗannan furuci ba. A nata ɓangaren, gwamnatin Paraguay ta nemi afuwa tare da nesanta kanta daga kalaman sanatar.
Shi ma Mbappé ya bayyana takaicinsa kan lamarin, yana mai cewa irin waɗannan kalamai ba su da gurbi a harkar wasanni ko al'umma.

0 $type={blogger}:
Post a Comment