Yadda Dakarun Haɗin Gwiwa Suka Ceto Ɗalibai Da Malaman Makaranta Da Kungiyar Ansaru Ta Sace A jihar Oyo.

Yadda Dakarun Haɗin Gwiwa Suka Ceto Ɗalibai Da Malaman Makaranta Da Kungiyar Ansaru Ta Sace A jihar Oyo.

Dakarun tsaron Najeriya sun fitar da hotunan aikin ceto da suka gudanar cikin sirri, wanda ya kai ga kubutar da ɗalibai da malamai da ƙungiyar ta'addanci ta Ansaru ta yi garkuwa da su a Jihar Oyo ranar 15 ga Mayu, 2026.

Rahoton Daily Trust ya ce aikin bincike da ceto, wanda aka kammala a ranar 9 ga Yuli, ya biyo bayan umarnin kai tsaye daga Shugaban Ƙasa. 


Hedikwatar Tsaro ta jagoranci aikin ta hanyar Rundunar Haɗin Gwiwar Hukumomin Tsaro, wadda ta haɗa da Sojojin Ƙasa da Sojojin Ruwa, Sojojin Sama da Rundunar 'Yan Sanda da Hukumar DSS da Hukumar NIA da Hukumar DIA da kuma Hukumar NSCDC.

An bayyana cewa an yi wa waɗanda aka ceto cikakken gwajin lafiya tare da ba su kulawar farko ta fuskar lafiyar kwakwalwa da ta tunani. 
Ana sa ran za a miƙa su ga Gwamnatin Jihar Oyo kafin a haɗa su da iyalansu.

0 $type={blogger}: