Hatsarin Kwale-Kwalen Mai Gudun gaske a Tekun Vietnam Ya Hallaka 'Yan Yawon Buɗe Ido 15 'Yan ƙasar Indiya.

Hatsarin Kwale-Kwalen Mai Gudun gaske a Tekun Vietnam Ya Hallaka 'Yan Yawon Buɗe Ido 15 'Yan ƙasar Indiya.

Akalla 'yan yawon buɗe ido mutun 15 ne 'yan ƙasar Indiya suka rasa rayukansu bayan wani kwale-kwalen mai gudun gaske ya kife a kusa da tsibirin Phu Quoc da ke kudancin Vietnam.

Rahotanni daga hukumomin Vietnam sun bayyana cewa kwale-kwalen na ɗauke da fasinjoji 32 'yan Indiya tare da ma'aikata huɗu lokacin da hatsarin ya afku yayin da yake dawowa daga tsibirin Hon May Rut Ngoai zuwa tashar jiragen ruwa ta An Thoi. 
An ceto mutane 21, yayin da waɗanda suka jikkata ke ci gaba da karɓar magani a asibiti.

Hukumomi sun ce har yanzu ba a tantance musabbabin hatsarin ba, kuma an ƙaddamar da bincike domin gano abin da ya haddasa kifewar kwale-kwalen.

Shaidu sun ce wasu jiragen ruwa da ke kusa sun yi gaggawar kai ɗauki kafin jami'an tsaron kan iyaka da rundunar sojojin ruwa da jami'an tsaron gabar teku su isa wurin. 
An kuma bayyana cewa wasu daga cikin fasinjojin sun makale a cikin kwale-kwalen bayan ya kife, lamarin da ya ƙara wahalar da aikin ceto.

Ofishin Jakadancin Indiya da ke Hanoi ya sanar da cewa ya buɗe cibiyoyin bayar da agajin gaggawa a Hanoi da Ho Chi Minh City domin taimaka wa iyalan waɗanda abin ya shafa tare da haɗa kai da hukumomin Vietnam.

Tsibirin Phu Quoc na daga cikin fitattun wuraren yawon buɗe ido a Vietnam, inda miliyoyin masu yawon buɗe ido ke ziyarta a kowace shekara. 
Wannan hatsari ya zo ne kusan shekara guda bayan wani mummunan hatsarin jirgin yawon buɗe ido a Ha Long Bay wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 39.

0 $type={blogger}: