Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da tsawaita wa'adin da ta bai wa jam'iyyun siyasa domin mika sunaye da bayanan 'yan takararsu na zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya na shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa wa'adin da aka tsara zai kare a ranar Asabar, 11 ga Yuli, 2026, yanzu an tsawaita shi zuwa tsakar daren ranar Talata, 14 ga watan Yuli, 2026.
INEC ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan bukatar da Majalisar Shawarar Jam'iyyun Siyasa (IPAC) ta gabatar, inda ta bayyana cewa wasu jam'iyyu ba su samu damar kammala loda sunaye da bayanan 'yan takararsu ta hanyar tsarin intanet na hukumar ba kafin karewar wa'adin farko.
Hukumar ta bayyana cewa tsawaita wa'adin na nuna kudurinta na tabbatar da adalci da bai wa dukkan jam'iyyun siyasa damar shiga tsarin zabe cikin gaskiya, tare da bin tanadin dokokin kasa.
INEC ta kuma bukaci jam'iyyun siyasa su yi amfani da karin kwanakin da aka ba su wajen kammala shigar da dukkan bayanan da ake bukata kafin sabon wa'adin ya cika.
Matakin ya zo ne bayan wasu jam'iyyu sun fuskanci kalubale wajen cika sharuddan mika sunayen 'yan takararsu cikin wa'adin farko.
A gefe guda kuma, jam'iyyar APC ta sanar da cewa ta kammala loda sunayen dukkan 'yan takararta 471 na zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment