Tsohon Sarkin ƙasar Qatar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani, ya rasu yana da shekaru 74 a duniya, kamar yadda Fadar Masarautar Qatar (Amiri Diwan) ta sanar a ranar Lahadi.
Sheikh Hamad ya jagoranci ƙasar Qatar daga shekarar 1995 zuwa 2013, inda aka yi masa yabo kan sauya fasalin ƙasar ta fuskar tattalin arziki da bunƙasa ababen more rayuwa da kuma ƙarfafa tasirin Qatar a siyasar duniya.
A shekarar 2013, ya miƙa mulki ga ɗansa, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, wanda ke ci gaba da mulkin ƙasar zuwa yanzu.
Fadar Masarautar Qatar ta tabbatar da rasuwarsa, sai dai ba ta bayyana musabbabin mutuwar ko kuma cikakken bayani kan shirye-shiryen jana'izarsa ba.
Ana sa ran hukumomin Qatar za su fitar da ƙarin bayani game da rasuwar tsohon sarkin nan ba da jimawa ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment