Adadin Mutanen da Suka Mutu Sakamakon Girgizar Kasa a Venezuela Ya Kai 4,333

Adadin Mutanen da Suka Mutu Sakamakon Girgizar Kasa a Venezuela Ya Kai 4,333

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa biyu da ta afku a ƙasar Venezuela a ranar 24 ga watan Yuni ya karu zuwa 4,333, a cewar Shugaban Majalisar Dokokin ƙasar, Jorge Rodriguez.

Rodriguez ya bayyana cewa mutane 16,740 sun jikkata, yayin da aka ceto mutane 6,462 daga wuraren da girgizar ta shafa. Ya kuma ce har yanzu ba a tantance gawarwakin mutane 315 ba, yayin da kusan mutane 17,000 suka rasa matsugunansu.

A cewarsa, gine-gine 856 ne suka lalace, ciki har da gine-gine 190 da suka rushe gaba ɗaya ko kuma suka samu mummunar matsalar tsari.

Gwamnatin ƙasar ta sanar da cewa mataimakiyar shugabar ƙasa mai riƙon kwarya, Delcy Rodriguez, za ta fara rabon gidaje 200 na farko ga waɗanda bala'in ya shafa daga mako mai zuwa.

Haka kuma, gwamnati ta kiyasta cewa ana buƙatar gina gidaje kusan 25,000 domin waɗanda suka rasa muhallansu, kuma tuni ta ware filaye kusan 40 domin aiwatar da sabbin ayyukan gidaje a yankunan Osma da Chuspa.

A halin yanzu, jami'an ceto na ci gaba da aikin bincike a wuraren da ake kyautata zaton akwai sauran mutanen da ka iya kasancewa a ƙarƙashin baraguzan gine-gine.

Rodriguez ta jaddada cewa za a ci gaba da ayyukan ceto, tana mai cewa har yanzu akwai fatan samun karin waɗanda suka tsira daga wannan mummunan bala'i.

0 $type={blogger}: