Mutane Biyu ne Suka Mutu, Yayin da Biyar Suka Jikkata Bayan Harbe-harben Dan Bindiga a Canada.

Mutane Biyu ne Suka Mutu, Yayin da Biyar Suka Jikkata Bayan Harbe-harben Dan Bindiga a Canada.

Mutane biyu ne aka bayar da rahotan sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka jikkata bayan wani ɗan bindiga ya buɗe wuta a lokacin wani shahararren bikin al'adun Latin da ake gudanarwa a birnin Toronto na ƙasar Canada.

'Yan sandan Toronto sun bayyana cewa sun isa wurin da lamarin ya faru inda suka tarar da mutane biyar da suka samu raunukan harbin bindiga. 
An tabbatar da mutuwar mutum biyu a wurin, yayin da ba a bayyana halin da sauran waɗanda suka jikkata suke ciki ba.

Mahukunta sun bukaci jama'a da su guji yankin domin bai wa jami'an tsaro damar gudanar da bincike. Har zuwa yanzu, ba a sanar da kama wani da ake zargi ba, kuma ba a bayyana musabbabin harin ba.

Firaministan Canada, Mark Carney, ya yi Allah wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin mummunan lamari. 
Ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da kuma waɗanda suka jikkata, tare da tabbatar da cikakken goyon bayansa ga jami'an tsaro domin cafke waɗanda ke da hannu a harin.

Bikin Al'adun na (Salsa on St. Clair) na daga cikin manyan bukukuwan al'adun Latin da ake gudanarwa a Toronto, inda dubban mutane ke halarta a kowace shekara. 
'Yan sanda sun ce za su ci gaba da fitar da bayanai yayin da bincike ke gudana.

0 $type={blogger}: