Tinubu Ya Amince da Kafa Sabon Bataliyar Sojoji a Jihar Kwara

Tinubu Ya Amince da Kafa Sabon Bataliyar Sojoji a Jihar Kwara

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa sabon bataliyar Rundunar Sojojin Najeriya a garin Omu-Aran da ke ƙaramar hukumar Irepodun a Jihar Kwara, domin ƙarfafa tsaro da yaƙi da matsalolin rashin tsaro a jihar.

An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Kwara, Mashood AbdulRafiu Agboola, ya fitar.

Sanarwar ta ce sabon sansanin sojojin zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan tsaro musamman a yankunan da ke fama da hare-haren 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran miyagun laifuka.

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yabawa Shugaba Tinubu kan amincewa da wannan mataki, yana mai cewa hakan zai ƙara wa jami'an tsaro ƙarfi ta hanyar samar da ƙarin sojoji da kayan aiki.

Ya kuma gode wa Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, bisa saurin aiwatar da buƙatar jihar na ƙarin jami'an soji.

Gwamnan ya ce sabon bataliyar zai taimaka wajen ƙarfafa yaƙi da ta'addanci da satar mutane tare da inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.

Haka kuma ya yaba da gudummawar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), Rundunar Sojojin Najeriya, Hukumar DSS, Rundunar 'Yan Sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro saboda haɗin gwiwar da suke yi wajen magance matsalolin tsaro.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba jami'an tsaro cikakken goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar Kwara.

0 $type={blogger}: