Akalla 'yan Najeriya 20 ne suka rasa rayukansu bayan wani kwale-kwale da ya yi lodin da ya wuce kima ya kife a cikin ruwan ƙasar Kamaru.
Rahotanni sun ce kwale-kwalen ya taso ne daga Garoua zuwa Yola, Jihar Adamawa, dauke da fasinjoji sama da 50 tare da sandunan ƙarfe da sauran kayan gini da ake kai wa Dasin da ke Karamar Hukumar Fufore.
Mazauna yankin sun bayyana cewa an shawarci masu jirgin su jinkirta tafiyar har zuwa safiyar ranar Talata saboda haɗarin tafiya da dare, amma suka yi watsi da wannan gargadi.
An ce cikin dare kwale-kwalen ya fada cikin wata guguwa mai ƙarfi, lamarin da ya sa ya kife. Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 18, inda aka yi musu jana'iza a Wuro Boki da ke Fufore, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda suka ɓace.
Tawagogin ceto daga Najeriya da Kamaru na ci gaba da aikin bincike, yayin da waɗanda suka tsira ke karɓar magani a asibitocin da ke garuruwan kan iyakar kasashen biyu.
Rundunar 'Yan Sandan Ruwa ta Jihar Adamawa ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne a cikin ruwan Kamaru, ba a yankin ruwan Najeriya ba.
Wannan mummunan lamari ya sake jawo hankali kan haɗarin amfani da kwale-kwalen katako masu ɗaukar kaya da fasinjoji fiye da ƙa'ida a hanyoyin kasuwanci tsakanin Najeriya da Kamaru.
Haka kuma gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnatocin jihohi su hana amfani da kwale-kwalen katako marasa ingantaccen tsaro domin kare rayukan al'umma.

0 $type={blogger}:
Post a Comment