Ƙasar Amurka Za Ta Sanar da Yarjejeniyar Makamashin Nukiliya da Saudiyya.

Ƙasar Amurka Za Ta Sanar da Yarjejeniyar Makamashin Nukiliya da Saudiyya.

Ana sa ran gwamnatin Amurka za ta sanar a yau Laraba wata muhimmiyar yarjejeniya ta haɗin gwiwa da Saudiyya kan samar da makamashin nukiliya domin amfanin farar hula.

Rahotanni sun ce gwamnatin Shugaba Donald Trump za ta rattaba hannu tare da hukumomin Saudiyya kan yarjejeniyar, wadda za ta bai wa ƙasar damar bunƙasa shirin makamashin nukiliya na farar hula tare da taimakon kamfanonin Amurka. Ana sa ran yarjejeniyar za ta samar wa masana'antar nukiliyar Amurka biliyoyin daloli.

A cewar rahotanni, yarjejeniyar wadda za ta yi aiki na tsawon shekaru 30 ta ƙunshi tanadin da zai bai wa kamfanonin Amurka damar gina cibiyar tace sinadarin uranium a Saudiyya, idan binciken haɗin gwiwa ya nuna akwai buƙatar hakan.

Sai dai wasu 'yan majalisar dokokin Amurka daga jam'iyyun biyu da kuma jami'an Isra'ila sun nuna adawa da shirin, saboda fargabar cewa fasahar za ta iya zama hanyar haɓaka makaman nukiliya a nan gaba, duk da cewa an ce an yi ta ne domin amfanin farar hula.

Ana sa ran za a gabatar da yarjejeniyar ga Majalisar Dokokin Amurka nan da kwanaki masu zuwa, amma ba lallai ne majalisar ta amince da ita ba kafin ta fara aiki.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ya sake ƙamari a Gabas ta Tsakiya. 'Yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran sun yi barazanar kakaba wa tashoshin jiragen ruwa na Saudiyya takunkumi, bayan sabon tashin hankalin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran. Haka kuma, Saudiyya da Houthi sun sake musayar hare-hare a makon da ya gabata, lamarin da ke barazana ga tsagaita wutar yaƙin da aka cimma a shekarar 2022.

Jami'an Amurka sun ce yarjejeniyar na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar makamashi tsakanin ƙasashen biyu tare da bunƙasa masana'antar nukiliyar Amurka.

0 $type={blogger}: