Sojoji Sun Ceto Mutumin Da Aka Yi Garkuwa Da Shi A Dajin Katsina, Tare da Rushe Sansanonin ’Yan Ta’adda.

Sojoji Sun Ceto Mutumin Da Aka Yi Garkuwa Da Shi A Dajin Katsina, Tare da Rushe Sansanonin ’Yan Ta’adda.

Dakarun Sojin Najeriya sun yi nasarar ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi, bayan an same shi a ɗaure da sarƙa a cikin dajin Fafu da ke jihar Katsina.

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin wani samame da dakarunta ke gudanarwa na kawar da maboyar ’yan ta’adda a ƙarƙashin aikin Operation CLEAN SWEEP.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar ranar Juma’a, 19 ga Yuni, 2026, dakarun Brigade ta 17 da Rundunar Musamman ta Division ta 8 sun kai farmaki kan wuraren da ake zargin ’yan ta’adda ke amfani da su a yankin Tuga da ke ƙaramar hukumar Matazu.

Sojojin sun samu goyon bayan bayanan sirri da sa ido da kuma hare-haren sama daga Operation FANSAN YAMMA, inda suka kwato dabbobi da suka haɗa da shanu 36 da tumaki 280 da jakuna biyu.

Bayan shiga cikin dajin Fafu, dakarun sun lalata sansanonin ’yan ta’adda da wuraren ajiyar kayayyaki bayan wani haɗin gwiwar harin sama da na ƙasa.

A yayin aikin, sojojin sun gano wata maboya da ake alakanta ta da wani fitaccen shugaban ’yan ta’adda. 
Sun gano gawarwaki biyu tare da ceto wani mutum mai suna Nura Yar’Adua, wanda aka same shi a ɗaure da sarƙa.

An ba wanda aka ceto agajin farko kafin a kai shi zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya Katsina domin samun kulawar lafiya.

0 $type={blogger}: