Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta sanar da cewa ta yi nasarar jigilar sojoji 198 zuwa ƙasar Gambiya domin ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya ƙarƙashin Rundunar Kungiyar ECOWAS a Gambiya (ECOMIG).
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Juma'a, ta ce an gudanar da jigilar ne ta amfani da jirgin C-130H na Rundunar Sojin Sama, a tafiya biyu da aka yi tsakanin ranar 26 zuwa 30 ga watan Mayu, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa an tura NIGCOY 11 domin maye gurbin NIGCOY 10, tare da jigilar kayan aiki na rundunar da kuma kayayyakin sojojin.
Rundunar Sojin ta ce wannan aiki ya nuna ƙarfin rundunar wajen kai sojoji cikin gaggawa zuwa ƙasashen waje domin tallafa wa zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a Gambiya da sauran ƙasashen yankin ECOWAS.
Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya ce ƙarfin sojin sama na taka muhimmiyar rawa wajen fuskantar sabbin barazanar tsaro a yankin.
Ya ce, "Kowane nasarar aikin jigilar sojoji ta sama tana ƙara tabbatar da ƙudurinmu na kare muradun Najeriya da tallafa wa zaman lafiyar yanki, da kuma tabbatar da cewa rundunarmu a shirye take koyaushe domin gudanar da duk wani aiki idan buƙata ta taso."
Rundunar ta kuma bayyana cewa wannan aiki ya nuna irin shirinta da ƙwarewarta wajen shiga ayyukan tabbatar da zaman lafiya na ƙasa da ƙasa, tare da ƙarfafa matsayin Najeriya a matsayin jagora wajen samar da zaman lafiya a yankin ECOWAS.
Najeriya na daga cikin manyan ƙasashen da ke bayar da gudunmawa ga aikin ECOMIG tun bayan kafa rundunar a shekarar 2017, bayan rikicin siyasa da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar Gambiya na 2016, lokacin da tsohon shugaban ƙasar Yahya Jammeh ya ƙi miƙa mulki bayan shan kaye.
Rundunar na ci gaba da tallafa wa tabbatar da dimokuraɗiyya da tsaro da gyaran fannin tsaro a Gambiya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment