Akalla mutane 3,700 ne suka mutu a ƙasashen Faransa da Belgium da Netherlands sakamakon tsananin zafin rana da ya mamaye sassan Turai a ƙarshen watan Yuni, kamar yadda hukumomin lafiya suka bayyana.
Faransa ce ta fi yawan mace-macen, inda aka samu mutane 2,025 da suka mutu sakamakon zafin rana.
Hukumomin lafiya sun ce mace-macen sun fi ƙaruwa a tsakanin mutanen da suka haura shekaru 45, yayin da adadin waɗanda suka mutu a gidajensu ya ƙaru da kashi 91 cikin 100 tsakanin ranar 22 zuwa 28 ga watan Yuni idan aka kwatanta da makon da ya gabata.
Hukumomi sun kuma yi gargaɗin cewa adadin mace-macen na iya ƙaruwa yayin da ake ci gaba da tattara bayanai.
A Belgium, an tabbatar da mutuwar ƙarin mutane kusan 1,200 tsakanin 18 zuwa 29 ga watan Yuni.
Daga cikinsu, fiye da 530 sun kasance masu shekaru 85 ko sama da haka, yayin da 180 kuma suka kasance ƙasa da shekaru 65. Ma'aikatar Lafiya ta ƙasar ta bayyana wannan adadin mace-mace a matsayin abin da ba a taɓa gani ba sakamakon zafin rana.
A Netherlands, hukumomi sun ce an samu kusan mutane 480 da suka mutu, inda mafi yawansu suka kasance masu shekaru sama da 80.
Masana sun ce zafin ranan, wanda ya ɗauki kusan daga 20 zuwa 28 ga watan Yuni, na ɗaya daga cikin mafi muni da Turai ta taɓa fuskanta.
Inda ya haifar da tangarda ga samar da wutar lantarki da lalacewar ababen more rayuwa da kuma cunkoso a cibiyoyin kiwon lafiya.
Masana kimiyyar sauyin yanayi sun bayyana cewa sauyin yanayi da ɗan Adam ke haddasawa ne ya ƙara tsananta wannan zafin rana, tare da nuna cewa irin waɗannan bala'o'i na iya ƙaruwa a nan gaba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment