Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya ƙaddamar da Asusun Bunƙasa Noma da Zuba Jari na Yankin Neja Delta, tare da rantsar da Kwamitin Daidaita Harkokin Noma da Zuba Jari domin haɓaka noma da jawo masu zuba jari a yankin.
Da yake jawabi a taron Bunƙasa Noma da Zuba Jari na Neja Delta da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Shettima ya bayyana cewa shirin wani muhimmin ɓangare ne na manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope Agenda, waɗanda ke da nufin bunƙasa noma da tabbatar da wadatar abinci da samar da ayyukan yi da kuma faɗaɗa tattalin arzikin Najeriya.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya jaddada cewa kafin man fetur ya zama ginshiƙin tattalin arzikin ƙasa, noma ne ke ciyar da Najeriya gaba. Saboda haka, ya ce lokaci ya yi da za a koma amfani da albarkatun ƙasa wajen gina tattalin arziki mai ɗorewa.
Ministan Raya Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh, ya buƙaci masu zuba jari su duba yankin Neja Delta a matsayin cibiyar noma mai dimbin damar bunƙasa, yana mai cewa noma na zamani da amfani da injuna ne makomar samar da abinci da ci gaban tattalin arziki.
Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Chiedu Ebie, ya ce hukumar na ci gaba da aiki daidai da manufofin gwamnatin tarayya wajen tabbatar da wadatar abinci da rage talauci da samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al'ummar yankin.
A nasa jawabin, Manajan Daraktan NDDC, Dakta Samuel Ogbuku, ya ce lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan dimbin damar noma da ke yankin Neja Delta, yana mai tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da samar da muhimman ababen more rayuwa domin tallafa wa ci gaban harkokin noma.
Shi ma Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ta bakin wakilinsa, ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar sauya noma daga na gargajiya zuwa noma na zamani domin ƙarfafa samar da abinci da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Masu halartar taron sun yi kira ga ƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zuba jari da kamfanoni masu zaman kansu domin jawo manyan jarin noma da mayar da yankin Neja Delta ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwancin noma a Najeriya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment