Gwamnatin Amurka ta amince da sayar wa ƙasar Saudiyya manyan makaman zamani masu linzami da sauran kayan aikin soja da darajarsu ta kai dala biliyan 1.96, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce yarjejeniyar ya ƙunshi "Makaman roka na zamani masu kai hari daidai kan abin da aka nufa (APKWS)." da sauran kayan tallafi domin ƙarfafa ƙarfin tsaron Saudiyya.
Ma'aikatar ta bayyana cewa kamfanin BAE Systems ne zai kasance babban mai gudanar da wannan yarjejeniyar.
Jami'an Amurka sun ce manufar sayar da makaman ita ce ƙarfafa tsaron Saudiyya a matsayin muhimmin ƙawarta a yankin Gabas ta Tsakiya, tare da taimaka mata wajen fuskantar barazanar tsaro a yanzu da kuma nan gaba.
Yarjejeniyar za ta bi matakan dubawa da amincewar Majalisar Dokokin Amurka kafin a kammala ta.

0 $type={blogger}:
Post a Comment