Yaki Ya Tsananta Tsakanin Amurka da Iran Yayin da Rikicin Ya Shiga Rana ta Biyar.

Yaki Ya Tsananta Tsakanin Amurka da Iran Yayin da Rikicin Ya Shiga Rana ta Biyar.

Yaƙi tsakanin Amurka da Iran ya shiga rana ta biyar, inda bangarorin biyu suka ci gaba da kai sabbin hare-hare, lamarin da ke kara tayar da hankalin kasashen duniya game da yiwuwar fadada yakin a Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun ce sojojin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan sansanonin soja da wuraren kariyar gabar teku da cibiyoyin makamai masu linzami da sauran muhimman wuraren soja na Iran domin rage karfinta na kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigar Hormuz.

A martaninta, Iran ta ce ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki kan wuraren da sojojin Amurka ke amfani da su a ƙasashen Jordan da Bahrain da Kuwait. 
Jordan ta sanar da cewa tsarin kariyarta ya yi nasarar kakkabo makamai masu linzami takwas da aka harba zuwa kasarta, yayin da Bahrain da Kuwait su ma suka kunna tsarin kariyar sararin samaniyarsusu saboda barazanar hare-haren jiragen marasa matuki.

Haka kuma, Amurka ta ci gaba da kakaba takunkumin ruwa kan tashoshin jiragen Iran, inda ta dakatar da wani jirgin dakon mai da ke kan hanyarsa zuwa tsibirin Kharg, cibiyar fitar da danyen man fetur ta Iran. 
Wannan mataki ya kara rage zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwan Hormuz, lamarin da ke tayar da fargaba kan samar da mai da kuma farashinsa a kasuwannin duniya.

A gefe guda, ana rahoton cewa Shugaban Amurka Donald Trump na nazarin yiwuwar fadada hare-haren soji kan wasu muhimman wuraren Iran. 
Sai dai gwamnatin Iran ta jaddada cewa ba ta da shirin komawa tattaunawa da Washington, tana mai gargadin cewa duk wani sabon hari zai fuskanci martani mafi tsanani.

A wani ci gaba kuma, Shugaba Trump ya sanar da cewa wata 'yar kasar Amurka mai suna Dena Karari, wadda ta makale a Iran tun karshen shekarar 2024, ta samu 'yanci kuma ta bar kasar cikin koshin lafiya.

Rikicin na ci gaba da haddasa damuwa ta fuskar jin kai, yayin da ake samun rahotannin jikkata fararen hula da lalacewar asibitoci da gidajen zama, tare da kira daga kasashen duniya da a dakatar da tashin hankalin domin kauce wa fadada yakin a yankin.

0 $type={blogger}: