Babban jami'in gwamnatin kasar Sin, Wang Huning, ya jagoranci wata tawaga zuwa Pyongyang, babban birnin Koriya ta Arewa, inda suka gudanar da tattaunawa da Jo Yong Won, babban jami'i a Jam'iyyar Ma'aikata mai mulkin kasar.
Ziyarar ta biyo bayan tafiyar da Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai Koriya ta Arewa a watan Yuni, inda shi da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un suka cimma yarjejeniyar kara karfafa dangantakar kasashen biyu.
A yayin tattaunawar, Wang Huning ya jaddada kudirin gwamnatin Sin na aiwatar da yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, musamman wajen fadada hadin gwiwa a fannonin diflomasiyya, tsaro, kasuwanci, al'adu da hulɗar jam'iyyun siyasa.
A nata bangaren, Koriya ta Arewa ta bayyana aniyarta ta kara karfafa sadarwa da hadin gwiwar dabaru da kasar Sin, yayin da bangarorin biyu suka tattauna hanyoyin inganta jin dadin al'umma da bunkasa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da al'adu.
Masana na ganin cewa yawaitar irin wadannan manyan ganawa na nuna kudirin kasashen biyu na kara karfafa dangantakarsu ta tarihi, duk da kusancin da Koriya ta Arewa ke yi da Rasha a 'yan shekarun nan.

0 $type={blogger}:
Post a Comment