An Kashe Mutum Ɗaya, Yayin da akayi Garkuwa Da Wani A Sabon Harin da 'Yan Ta'adda Suka Kai Jihar Kwara.

An Kashe Mutum Ɗaya, Yayin da akayi Garkuwa Da Wani A Sabon Harin da 'Yan Ta'adda Suka Kai Jihar Kwara.

Akalla mutum daya ne ya rasa ransa, yayin da aka yi garkuwa da wani, sannan wasu da dama suka jikkata bayan wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne suka kai hari garin Wande da ke ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara a daren Laraba.

Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin garin ne tare da bude wa mazauna yankin wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda kafin su tsere da wani da suka sace.

Wani da ya tsira daga harin ya ce maharan sun buge shi da gindin bindiga a kai, lamarin da ya jikkata shi sosai. Haka kuma, an garzaya da wani da aka harba zuwa asibitin Igbaja domin samun kulawar likitoci.

Mazauna yankin sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da tabarbarewar tsaro a Kudancin Kwara, suna cewa hare-haren da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke kaiwa sun tilasta wa al'ummomi da dama barin gidajensu.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa ana zargin maharan su ne 'yan ta'addan da jami'an tsaro suka fafata da su a garin Yaru tun da safiyar Laraba, kafin su tsere zuwa Wande inda suka kai wannan hari.

Sabon harin ya sake tayar da hankalin jama'a kan matsalar rashin tsaro da ke ƙara kamari a Kudancin Jihar Kwara, duk da ci gaba da ayyukan jami'an tsaro na yaƙi da 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane.

0 $type={blogger}: