Adadin mutanen da suka mutu sakamakon mummunar girgizar ƙasa biyu da ta afku a Venezuela ya karu zuwa 2,954, kamar yadda hukumomi suka sanar a ranar Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa adadin mamatan ya ƙaru da sama da 300 idan aka kwatanta da alkaluman da aka fitar ranar Juma'a.
Haka kuma, sama da mutane 16,000 sun jikkata tun bayan girgizar ƙasar da ta auku a ranar 24 ga watan Yuni.
Girgizar ƙasar ta rushe gine-gine da dama na gidaje da kasuwanci, yayin da dubban mutane har yanzu ake ci gaba da neman su a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen.
Ma'aikatan Hukumar Kare Fararen Hula ta Venezuela da jami'an kashe gobara da masu aikin sa-kai da sauran jami'an agaji na ci gaba da gudanar da aikin ceto domin gano waɗanda suka tsira da fitar da gawarwaki da kuma kai tallafi ga mutanen da bala'in ya shafa.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da aikin ceto da bayar da agajin gaggawa ga dubban iyalan da wannan mummunar girgizar ƙasa ta shafa, wadda ake ganin tana daga cikin mafi muni a tarihin ƙasar Venezuela na baya-bayan nan.

0 $type={blogger}:
Post a Comment