Darajar naira ya sake faduwa a kasuwar canji ta bayan fage (parallel market), inda aka sayar da dala daya kan N1,403, idan aka kwatanta da N1,385 da aka sayar a ranar Laraba.
Haka kuma, naira ta kara yin rauni a Kasuwar Musayar Kudin Waje ta Najeriya (NFEM), inda farashin musayar kudin ya tashi zuwa N1,371.4 kan dala daya, daga N1,369 da aka musanya a ranar Laraba, kamar yadda bayanan Babban Bankin Najeriya (CBN) suka nuna.
Sakamakon haka, tazarar da ke tsakanin farashin dala a kasuwar bayan fage da ta hukuma ta karu zuwa N31.6 kan dala, daga N16 da aka samu a ranar da ta gabata.
A lokaci guda, yawan hada-hadar musayar kudaden waje a kasuwar hukuma ya ragu da kashi 4.9 cikin 100, inda ya sauka zuwa dala miliyan 85.5, daga dala miliyan 90.3 da aka samu ranar Laraba.
Faduwar darajar naira na zuwa ne a daidai lokacin da hauhawar farashin kayayyaki ke sake karuwa a Najeriya, lamarin da ke kara jefa damuwa kan tattalin arzikin kasar da kuma dorewar darajar kudin naira.

0 $type={blogger}:
Post a Comment