Daruruwan dubban masu makoki ne suka mamaye titunan birnin Tehran a ranar Asabar yayin da aka fara jana'izar tsohon Jagoran Kolin Iran, Ayatullah Ali Khamenei.
Mahukuntan Iran sun ce ana sa ran sama da mutum miliyan 10 za su halarci bukukuwan jana'izar da za su gudana a sassa daban-daban na ƙasar cikin mako guda.
An fara taron ne a Babban Masallacin Imam Khomeini Mosalla, inda dubban mutane sanye da bakaken kaya suka taru domin yi masa bankwana.
Khamenei mai shekaru 86 ya rasu ne sakamakon harin hadin gwiwar Amurka da Isra'ila a farkon yakin da aka gwabza da Iran a watan Fabrairu. Haka kuma wasu daga cikin 'yan uwansa da suka mutu a harin suna cikin wadanda ake yi wa jana'izar.
Domin saukaka wa bakin da suka yi tattaki daga sassan ƙasar, gwamnati ta bude sama da makarantu 5,000 tare da dubban ajujuwa domin zama wuraren saukar baki.
Hakazalika, wakilai daga ƙasashe fiye da 100 sun halarci tarukan girmamawa na hukuma, abin da ke nuna muhimmancin sauyin shugabanci a Iran ga kasashen duniya.
Za a ci gaba da jana'izar a Tehran har zuwa ranar Litinin, kafin a wuce da gawarsa zuwa birnin Qom, daga nan zuwa Iraki, sannan a karshe a binne shi a birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran.
An kuma tsaurara matakan tsaro a Tehran, inda jami'an tsaro suka bazama domin tabbatar da zaman lafiya da kuma kula da dimbin masu halartar jana'izar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment