Jami'an Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi sun kama matasa 25 a wani samame da suka kai wani otel da ke garin Argungu bisa zargin aikata ayyukan da suka saba wa tarbiyya.
Daraktan Shari'a na Hukumar Hisbah, Sirajo Kamba, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar. Ya ce an gudanar da samamen ne a ranar 3 ga watan Yuli a matsayin wani bangare na kokarin hukumar na yaki da munanan dabi'u da kuma inganta kyawawan halaye a fadin jihar.
A cewarsa, cikin wadanda aka kama akwai maza 12 da mata 13.
Kamba ya ce za a gudanar da cikakken bincike kan wadanda ake zargin bisa tanadin doka, yana mai cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci matakan shari'a da suka dace.
Ya kara da cewa wannan samame na cikin shirye-shiryen Hukumar Hisbah na tabbatar da zaman lafiya, tsafta da kuma kare kyawawan dabi'u a Jihar Kebbi.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana takamaiman laifukan da ake zargin matasan da aikata ba, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

0 $type={blogger}:
Post a Comment