Wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne tare da hadin gwiwar mayaƙan Tuareg masu neman ballewa sun kaddamar da sabbin hare-hare a lokaci guda a wasu garuruwa da dama na kasar Mali da sanyin safiyar Asabar.
Rahotanni sun ce hare-haren sun fara ne da misalin karfe 5:00 na safe, inda suka kai farmaki kan sansanonin sojoji da kuma gidan yari da ke Kenieroba, kusa da babban birnin kasar, Bamako.
Garuruwan da harin ya shafa sun hada da Gao da Anefis da Aguelhok da Sevare.
Kakakin kungiyar Azawad Liberation Front (FLA), Mohamed Elmaouloud Ramadane, ya ce mayaƙansu sun kwace wasu sansanonin sojoji a garin Anefis, amma har yanzu ana ci gaba da gwabza fada a wasu sassan garin.
Wani mazaunin Anefis ya bayyana cewa mayaƙan sun shiga garin, yayin da sojojin Mali ke ci gaba da kokarin kare sansaninsu.
Rahotanni sun nuna cewa garuruwan Anefis da Aguelhok na daga cikin wuraren karshe da sojojin Mali ke ci gaba da rike da su a yankin Kidal, bayan manyan hare-haren da aka kai a karshen watan Afrilu.
A garin Gao kuwa, mazauna sun ce sun ji karar bindigogi da fashe-fashe masu karfi kusa da wani sansanin sojoji.
Haka kuma a Sevare, an ji fashe-fashe tun da sassafe kafin a ga jiragen yakin sojoji suna shawagi a sararin samaniya.
An kuma kai hari gidan yarin Kenieroba, inda ake tsare da wadanda ake zargi da alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda da sauran fursunoni.
Wani fursuna ya shaida wa AFP cewa sun fake a karkashin gadajensu saboda ci gaba da harbe-harben.
Wannan sabon hari na zuwa ne sama da watanni biyu bayan wasu makamantan hare-hare da suka yi wa gwamnatin mulkin soja ta Mali mummunar illa, ciki har da kashe ministan tsaron kasar.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyukan yaki a wuraren da abin ya shafa, yayin da ba a fitar da adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata a hukumance ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment