Mutane biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 34 suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi a wani asibiti da ke garin Ludwigslust, a arewa maso gabashin ƙasar Jamus, da safiyar yau Alhamis.
Rahotanni sun ce gobarar ta fara ne daga ɗakin wani mara lafiya kafin ta bazu zuwa rufin sashen daukar hoton jiki (radiology) na asibitin.
Ma'aikatan ceto sun kwashe marasa lafiya 82 daga cikin ginin yayin da hayaƙi mai yawa ya mamaye asibitin.
Yawancin waɗanda suka jikkata sun shaƙi hayaƙi ne, inda jami'ai suka ce babu wanda ke cikin mawuyacin hali.
Sama da jami'an kashe gobara da na agajin gaggawa 100 ne suka halarci wurin domin shawo kan lamarin, kuma daga bisani sun samu nasarar kashe gobarar.
An rufe sashen karɓar masu gaggawa na asibitin na ɗan lokaci, amma daga baya aka sake buɗe shi. Hukumar gudanarwar asibitin ta ce za a ci gaba da aiki a sassan da gobarar ba ta shafa ba bayan kammala binciken tsaro.
'Yan sanda sun fara bincike domin gano musabbabin gobarar, wanda har yanzu ba a tantance ba. Asibitin shi ne kaɗai ke ba da manyan ayyukan lafiya a garin Ludwigslust da ke jihar Mecklenburg-Vorpommern ta Jamus.

0 $type={blogger}:
Post a Comment