Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da shirinta na maye gurbin kayan masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ke sawa da kayan Gargajiya da ake ƙerawa a cikin ƙasar, a wani ɓangare na manyan sauye-sauyen da ake yi wa shirin.
Ministan Matasa, Ayodele Olawande, ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da ya yi a tashar Channels Television a ranar Alhamis. Ya ce matakin na da nufin bunƙasa masana'antun cikin gida da kuma tabbatar da cewa kuɗaɗen gwamnati na tallafa wa tattalin arzikin Najeriya.
Ya bayyana cewa ana samar da kayan Gargajiya a jihohi irin su Ogun da Kwara, yana mai cewa gwamnati na son amfani da kayayyakin da ake ƙera a gida domin ƙarfafa masana'antar masaku ta Najeriya.
Ministan ya kuma ce a ƙarƙashin sabon tsarin, za a riƙa tura masu yi wa ƙasa hidima wuraren aiki bisa la'akari da fannin da suka karanta. Misali, waɗanda suka kammala karatun koyarwa za a tura su makarantu, yayin da sauran za a tura su wuraren da suka dace da ƙwarewarsu.
Dangane da batun tsaro, Olawande ya ce gwamnati na nazarin yiwuwar tura matasa zuwa yankunan da suka yi karatu ko suka saba da su, domin rage matsalolin tsaro da kuma sauƙaƙa tsarin tura masu hidimar.
Sai dai ya musanta rahotannin da ke cewa za a cire rundunar soji daga cikin tsarin NYSC, yana mai cewa sojoji za su ci gaba da ba da kariya ga masu yi wa ƙasa hidima, yayin da jagorancin gudanarwar shirin zai koma hannun farar hula.
Sabbin sauye-sauyen sun biyo bayan amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya da wani gagarumin garambawul ga shirin NYSC, wanda shi ne na farko tun bayan kafa shirin a shekarar 1973. Haka kuma, an umurci Babban Lauyan Tarayya da Ma'aikatar Matasa da su gyara dokar NYSC domin ta dace da sabbin sauye-sauyen.

0 $type={blogger}:
Post a Comment