Farashin danyen man fetur ya sake faduwa a rana ta uku a jere bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da Iran a birnin Doha na ƙasar Qatar, lamarin da ya rage fargabar katsewar safarar mai ta mashigin ruwan Hormuz.
Farashin danyen man Brent ya ragu da kashi 1.48 cikin ɗari zuwa dala 70.51 kan ganga, yayin da na West Texas Intermediate (WTI) na Amurka ya sauka da kashi 1.55 cikin ɗari zuwa dala 67.52 kan ganga, mafi ƙarancin farashinsa tun ƙarshen watan Fabrairu.
Qatar ta bayyana cewa tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ta samu ci gaba mai kyau kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Yuni, duk da cewa ba a kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin ba. Ana sa ran za a ci gaba da tattaunawar bayan kammala jana'izar marigayi Jagoran Addinin Iran.
Masana sun ce ci gaba da zirga-zirgar jiragen dakon mai ta mashigin Hormuz, sakin man fetur daga rumbunan ajiyar gaggawa, da kuma ƙarancin buƙatar mai daga China sun taimaka wajen saukar farashin.
Sai dai Iran ta yi gargadin cewa duk wani yunkurin Amurka na tsoma baki a mashigin Hormuz zai fuskanci martani cikin gaggawa da ƙarfi.

0 $type={blogger}:
Post a Comment