Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta fara rajistar aikin Hajjin shekarar 2027, inda ta sanya Naira miliyan 7.5 a matsayin kudin farko da masu niyyar zuwa aikin Hajji za su biya.
Hukumar ta kuma sanar da cewa rajistar za ta rufe cikin kwanaki 87, tare da kira ga masu sha'awar zuwa Hajjin da su gaggauta kammala rajistarsu kafin wa'adin ya cika.
Babban Daraktan Hukumar, Ahmed Labbo, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da jami'an hukumar na shiyyoyi daga kananan hukumomi 27 na jihar a hedikwatar hukumar da ke Dutse.
Labbo ya ce fara rajistar da wuri ya biyo bayan umarnin Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) da kuma hukumomin Saudiyya domin ba da damar tsara aikin Hajji cikin lokaci.
Ya bayyana cewa gwamnatin Saudiyya ta sanya watan Satumba a matsayin wa'adin karshe na rajistar maniyyata daga dukkan kasashen duniya, saboda haka ya zama wajibi masu niyyar zuwa Hajji su tabbatar da gurabensu tun da wuri.
Ya umarci jami'an shiyyoyi da su kara wayar da kan al'umma tare da tabbatar da cewa an cike dukkan guraben Hajjin da aka ware wa jihar kafin wa'adin ya kare.
Labbo ya ce biyan kudin farko da wuri zai taimaka wa hukumar wajen shirya harkokin sufuri, masauki, abinci da sauran tsare-tsaren da suka shafi aikin Hajji a Saudiyya.
Ya kuma bayyana cewa aikin Hajjin 2026 ya fuskanci kalubale sakamakon jinkirin biyan kudi da kuma rashin kammala takardu, yana mai jaddada cewa hukumar ba ta son sake fuskantar irin wadannan matsaloli a Hajjin 2027.
Hakazalika, Darakta Janar din ya yabawa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa ci gaba da ba hukumar goyon baya, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen gudanar da ayyukan Hajji cikin nasara a jihar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment